logo

HAUSA

Liang Jianying, injiniya ce da ta jagoranci kera jiragen kasa a yayin da take da shekaru 23, da jiragen kasa masu sauri a yayin da take da shekaru 34

2024-04-23 09:54:14 CMG Hausa

A shekarar 2006, kamfanin Sifang da Liang Jianying ke aiki a cikin sa, ya fara nazari da kera jirgin kasa mai saurin tafiya, wanda ke gudu da saurin kilomita 300 a sa'a guda. Liang Jianying ta yi aiki a matsayin babbar mai tsare-tsare a wannan aiki. 

Bayan namijin kokarin da suka yi, a watan Disamba na shekarar 2007, tawagar Liang Jianying ta yi nasarar samun ci gaba a fannin fasahar karfin sarrafa iska, da wasu muhimman fasahohi da dama, ta hakan kuma aka samar da jirgin kasa na farko mai gudun kilomita 350 a cikin sa'a guda a kasar Sin.

A shekarar 2008, kamfanin Sifang na CRRC ya fara yin kirkire-kirkire da kansa, don nazari da kera jirgin kasa mai sauri na CRH380A. Liang Jianying ta sake zama babban mai tare-tsare a wannan aiki. Bisa shirin da aka yi, matsakaicin saurin gudu na CRH380A zai kai kilomita 380 a cikin awa guda, irin matakin saurin da ba shi da wani misali a duniya.

Domin fahimtar yanayin jiragen kasa masu sauri a yayin da suke tafiya cikin sauri, Liang Jianying ta jagoranci tawagarta zuwa wurare daban-daban na kasar Sin, don gudanar da gwaje-gwajen bincike na kimiyya masu yawa. A cewarta, "Idan ba za mu iya zama mafi kyau a duniya ba, za mu nemi afuwar kasar mu da zamani."

Ta wannan hanyar, Liang Jianying ta jagoranci tawagar don kammala gwajin layi na shekaru biyu, wadan ya hada da yin kididdiga fiye da sau 450, da gwaje-gwajen kasa fiye 1,050, da ma gwaje-gwajen hanyoyi fiye da 2,800. A shekarar 2010, an yi nasarar kaddamar da jiragen kasa masu saurin gudu na CRH380A, wanda kuma ya yi gudu mafi sauri a gwajin jiragen kasa a duniya bisa gudun kilomita 486.1 a cikin sa'a guda! Wannan nasarar da aka samu ta farantawa al'ummar kasar baki daya, domin kuwa saurin da kasar Sin ta yi ya girgiza duniya.

Liang Jianying ba ta tsaya kan aikin ba, inda ta jagoranci tawagarta wajen ci gaba da shiga sababbin ayyukansu na yin kirkire-kirkire kan fasaha akai-akai. A cewar ta binciken kimiyya kamar hawa kololuwa ne. A wannan lokacin, Liang Jianying ba wai kawai burinta shi ne neman cimma nasara ba, har ma tana mayar da burin al'ummar kasar Sin baki daya a matsayin babban nauyin dake wuyan ta.

A shekarar 2013, aka kaddamar da aikin raya jirgin kasa mai sauri na "Fuxing", kuma Liang Jianying ta yi niyyar samun sabuwar nasara kan fasahar jirgin kasa mai sauri.

Daga tabbatar da samfurin jiragen kasa zuwa aikin na karshe, an gudanar da gwaje-gwajen layin godo har fiye da sau 2,300, tsawon gwaje-gwajen ya kai kilomita dubu 610, kwatankwacin da'ira 15 a kewayen equator na duniya, wanda ya dauki tsawon shekara daya da rabi.

Lokacin da aka kaddamar da jirgin kasa na "Fuxing", karfin juriya na dukkan abin hawan ya ragu da kashi 12%, an kuma rage amo da ma’aunin dB 4 zuwa 6, kana ma'aunin santsi ya kai matsayi mai kyau ... Wannan ya nuna cewa, aikin raya jiragen kasa masu sauri ya kai wani sabon matsayi. A shekarar 2017, jirgin kasa na "Fuxing" ya fara aiki a hukumance, lamarin da ya sa ci gaban zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin ya sake jawo hankulan duniya. Har ila yau a wancan lokaci, jiragen kasa masu sauri na kasar Sin su ma sun kasance a sahun gaba a duniya.

A ranar 17 ga watan Oktoba na shekarar 2023, jirgin kasa mai sauri na G1137 da kasashen Sin da Indonesia suka kera tare, ya tashi daga tashar Halim da ke birnin Jakarta zuwa birnin Bandung na kasar Indonesia, bisa matsakaicin saurin tafiya na kilomita 350 a cikin sa'a guda, kuma mafi saurin lokacin tafiya tsakanin wuraren biyu ya ragu daga sa'o'i 3.5 zuwa mintuna 40.

Layin dogo na jirgin kasa mai sauri na Jakarta–Bandung, shi ne layin dogo mai sauri na farko a kudu maso gabashin Asiya, wanda ya nuna yadda kasar Indonesiya ta shiga zamanin jirgin kasa mai sauri, kuma shi ne karon farko da kasar Sin ta fitar da layin dogo mai sauri zuwa kasashen waje, wanda kuma ya nuna babbar nasarar da kasashen Sin da Indonesiya suka cimma wajen raya shawarar “Ziri daya da hanya daya”tare. Liang Jianying da tawagarta, sun baiwa duniya mamaki, kan fasahohi masu ci gaba a jirgin kasa na "Fuxing".

Liang Jianying ta ce, “Yanzu, mun yi imani da cewa, muna iya fitar da fasahar jirgin kasa mai sauri zuwa dukkanin duniya, saboda irin taimakon da kasarmu ke bayarwa bisa manyan tsare-tsare, kana kuma yankin kasarmu mai fadi, da bukatun al’umma masu yawa a fannin zirga-zirga, dukkansu sun ba mu damar karfafa yin kirkire-kirkire kan fasaha."

A shekarar 2016, Liang Jianying da tawagarta sun tabbatar da sabon burinsu, wato nazari, da kuma kera jirgin kasa mai tafiya da karfin maganadisu mai saurin kilomita 600 a cikin sa'a guda.

Bayan kokarin da suka yi na shekaru 5, a ranar 20 ga watan Yuli na shekarar 2021, an yi nasarar kaddamar da tsarin zirga-zirgar jiragen kasa masu tafiya da karfin maganadisu mai saurin kilomita 600 a cikin sa’a guda, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin ta sami cikakkiyar kwarewa, kuma ta mallaki jerin fasahohin kera irin wannan jirgin kasa, da ma karfin aikin injiniya a fannin.

A watan Satumba na shekarar 2022, jirgin kasa mai tafiya da karfin maganadisu mai sauri, ya zama abin da ya fi daukar hankali a kafofin watsa labaran duniya, inda ake yabawa da shi da yi masa taken "mafi sauri a saman kasa", wanda ya sake nuna babban ci gaba na aikin raya layin dogo na kasar ta Sin.

Game da daukakar ta daga ma’aikaciya a fannin fasaha zuwa “fitacciyar injiniya ta kasa”, Liang Jianying ta ce, dalilin da ya sa ta samu irin wannan nasarar shi ne, ta samu wata dama mai kyau, wato kasarta ta Sin na kokarin bunkasa ayyukan sufurin jiragen kasa masu sauri, hakan ya sa aka ba ta dandamali na nuna kwarewarta, kuma tawagarta ce ta ba ta kwarin gwiwa wajen shawo kan duk matsalolin da take fusanta.