logo

HAUSA

Shugaban Faransa ya nanata adawarsa ga hare-haren da Isra’ila ke shirin kai wa Rafah

2024-04-23 11:21:37 CMG Hausa

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya bayyana adawar da kasarsa ke yi da hare-haren da Isra’ila ke shirin kaiwa birnin Rafah, dake kudancin zirin Gaza, yana mai kira ga Falasdinu da Isra’ila da su gaggauta tsagaita bude wuta.

Shugaba Emmanuel Macron ya nanata hakan ne yayin da yake tattaunawa ta wayar tarho da firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu a jiya Litinin. 

Fadar shugaba na Faransa ta fitar da sanarwa a jiya cewa, yayin tattaunawar ta wayar tarho, Macron ya bayyana cewa, ana fuskantar tsanantar yanayin jin kai a zirin Gaza, kuma fararen hula dake wurin sun dade suna cikin mawuyacin halin da ba za a iya amincewa da shi ba. Ya kara da cewa, hare-haren da Isra’ila ke shirin kaiwa Rafah ba za su haifar da komai ba illa tabarbarewar yanayin zirin Gaza da kara tsanantar rikicin. A sa’i daya kuma, Macron ya bukaci a tabbatar da ganin tallafin jin kai mai yawa ya shiga zirin Gaza.(Safiyah Ma)