logo

HAUSA

Bloomberg: Yada Jita-jitar “Wuce Gona Da Iri” Wajen Samar Da Hajojin Sin Da Ba Sa Gurbata Muhalli Zai Illata Sauyin Tsarin Makamashin Duniya

2024-04-23 14:13:38 CMG Hausa

A kwanan baya, kamfanin dillancin labarai na Bloomberg ya buga labarin da ke cewa, gwamnatocin Amurka da na kasashen Turai suna son ware kayayyakin da ba sa gurbata muhalli na kasar Sin, inda ya ce irin wannan ra’ayi na ba da kariya a fannin tattalin arziki zai jinkirta yunkurin sauya tsarin amfani da makamashi a duniya.

Labarin ya nakalto wani rahoto da Hukumar Kula da Makamashin Iska ta Duniya ta fitar kwanan nan dake cewa, yawan sabbin injuna masu farfela dake amfani da karfin iska da aka harhada a duk duniya, ya kai gigawatt 117 a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 50% bisa na makamancin lokacin a shekarar 2022. Amma idan ba a yi la’akari da sassan na’urorin da kasar Sin ke samarwa ba, karfin samar da kayayyakin a sauran yankuna na duniya ya karu da gigawatt 0.088 ne kadai idan aka kwatanta da na shekarar 2020.

Labarin ya bayyana cewa, don sake fasalin tsarin makamashin duniya, ya zama dole a kara zuba jari, da yin maraba da goyon bayan gwamnatoci daga kasashe daban-daban, ciki har da Sin, da Amurka, da ma kasashen Turai, maimakon haifar da yakin cinikayya mai barna. Haka kuma, idan aka kera samfuran bisa ma'aunin da ake bukata don hana dumamar yanayi, to, hakan ba wuce gona da iri wajen samar da hajoji ba ne, sai dai ainihin adadin da duniya ke bukata. (Mai fassara: Bilkisu Xin)