logo

HAUSA

Yankin masana’antu da Sin ta gina a Habasha ya samu kudin shiga dala miliyan 28 cikin watanni 9

2024-04-23 11:12:07 CMG Hausa

An samu kimanin dala miliyan 28 na kudin shiga a cikin watanni 9, daga fiton kayayyakin da aka samar a yankin masana’antu na Kombolcha da Sin ta gina a Habasha.

Babban manajan yankin masana’antu na Kombolcha (KIP) Ahmed Seid, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar cewa, an samu kudin ne daga kayayyakin da aka samar a cikin yankin na KIP cikin watanni 9 na farkon shekarar kudi ta 2023/2024 da ake ciki yanzu haka a kasar Habasha, wadda aka fara daga ranar 8 ga watan Yulin 2023.

Ahmed Seid ya kara da cewa, a cikin wannan lokaci, yankin na KIP ya samarwa mazauna sama da 850 guraben ayyukan yi.

Kamfanin gine-gine na kasar Sin na CCECC ne ya gina tare da kaddamar da yankin masana’antun na Kombolcha a watan Yulin 2017, a matsayin wani bangare na burin gwamnatin Habasha na bunkasa tattalin arzikinta da mayar da kasar zuwa cibiyar samar da kayayyaki a nahiyar Afrika. (Fa’iza Mustapha)