logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen kasar Nijar yayi wata ganarwa tare da jakadar Amurka a Nijar kuma makaranba

2024-04-23 13:48:15 CMG Hausa

A ranar jiya Litinin 22 ga watan Afrilun shekarar 2024, ministan harkokin waje da ‘yan Nijar da ke ketare, Bakary Yaou Sangare ya gana da jakadar Amurka da ke Nijar madam Kathleen Fitzgibbon a fadarsa da ke birnin Yamai. Inda jami’an biyu suka maida hankali kan  batutuwan da dama na lokaci.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Ita dai wannan ganawa ta zo daidai da lokacin da kasar Amurka take fuskantar  kalubale da matsalin lamba daga al’amomin kasar Nijar, na da ta kwashe sojojinta daga wannan kasa da ke yammacin Afrika. Ta haka ne, shugabar diplomasiyar Amurka a Nijar ta samu rakiyar madam Maria Barron darektar tawagar kungiyar USAID da ke Nijar a yayin wannan ganawa tare da shugaban diplomasiyar kasar Nijar. Ministan harkokin wajen kasar Bakary Yaou Sangare, tare da jakadar kasar Amurka tattaunawar ta maida hankali kan batun janyewar dakarun Amurka daga Nijar. 

A yayin wannan musanya tare da babbar jami’ar kungiyar USAID, an maida hankali kan aiwatar da ci gaban dangantaka musammun ma kan sanya hannu nan gaba kan sabuwar yarjejeniya da za ta maye gurbin wanda aka sanyawa hannu da zata kare a cikin watan Satumban shekarar 2024.

Haka kuma tattaunawar ta gudana a gaban idon manyan jami’ai da kwararru na ma’aikatar harkokin wajen kasar Nijar da kuma kusoshin da ke aiki tare da jakadar Amurka da ke Nijar madam Kathleen Fitzgibbon.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.