Xi ya yi rangadi a birnin Chongqing dake kudu maso yammacin kasar Sin
2024-04-23 14:25:26 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin kuma sakatare janar na kwamitin kolin JKS, Xi Jinping, ya yi rangadi a birnin Chongqing dake kudu maso yammacin kasar, daga jiya Litinin zuwa yau Talata.
Yayin rangadin, Xi Jinping ya kai ziyarar cibiyar jigilar kayayyaki ta kasa da kasa, da unguwar mazauna dake yankin Jiulongpo, da kuma cibiyar tafiyar da harkokin birnin ta zamani.
Ya kuma gano kokarin da gwamnatin birnin ke yi wajen gaggauta raya sabuwar cibiyar cinikayya daga kan tudu zuwa teku ta kasa da kasa dake yammacin kasar, da aiwatar da ayyukan sabunta birnin, da tabbatar da kyautata rayuwar jama’a, da ma yunkurin zamanantar da tsarin tafiyar da harkokin birnin. (Fa’iza Mustapha)