logo

HAUSA

Taimakon kasar Sin na ingiza ci gaba a nahiyar Afrika

2024-04-23 19:58:57 CMG Hausa

Kafofin yada labarai a kasar Habasha sun ruwaito a jiya cewa, yankin masana’antu na Kombolcha (KIP) da kasar Sin ta gina a kasar, ya samar da kimanin dala miliyan 28 na kudin shiga daga fiton kayayyaki zuwa ketare, cikin watannin 9 na farkon shekarar kudi ta kasar ta (2023/2024) da ta fara daga ranar 8 ga watan Yulin 2023.

Wannan ci gaba abun burgewa ne matuka, ganin yadda dukkan abubuwan da aka fitar, an samar da su ne a harabar yankin na KIP na kasar Habasha. Samar da yankin da kamfanin CCECC na kasar Sin ya gina, wani bangare ne na burin Habasha na zama cibiyar samar da kayayyaki a nahiyar Afrika, kuma da alama ta dauki hanyar cimma wannan buri nata, da taimakon kasar Sin.

Yayin da ake fama da hauhawar farashin kayayyaki da ma raguwar darajar kudaden kasashe musamman na Afrika, masana na cewa samar da kayayyaki a cikin gida, wata ingantacciyar dabara ce ta shawo kan matsaloli da dama. Tabbas Habasha ta samarwa kanta mafita, godiya ga kasar Sin.  Zan bada misali da wasu batutuwa 3.

Na farko, samar da kayayyaki a cikin gida. Yadda wannan yanki na KIP ke samar da kayayyaki a cikin gida, tabbas zai ragewa al’ummar kasar radadin hauhawar farashin kayayyaki. Ba su kadai ba ma, har da kasashe makwabta da nahiyar baki daya. Wannan lamari zai kara inganta kyautata rayuwar jama’a.

Na biyu, fiton kayayyaki. Wannan zai bunkasa karfin kasar na shiga kasuwannin duniya da ma kara haskata a dandalin kasa da kasa. Haka kuma zai kai ga bunkasa lamarin da zai bata karin damarmakin samun karin ci gaba ta fuskar kasuwanci da ababen more rayuwa tare da janyo jarin waje.

Na uku, samar da guraben ayyukan yi.  Cikin watannin 9, wannan yankin masana’atu da Sin ta gina, ya samar da karin guraben ayyukan yi sama da 850 ga mazauna wurin. Daya daga cikin manyan abubuwan dake haifar da rashin ci gaba kasa da ma rikice-rikice shi ne yawaitar masu zaman kashe wando, amma da zarar aka samu ayyukan yi, to ya kan toshe kafofi da dama masu tarnaki  ga ci gaban tattalin arziki da zaman takewar al’umma.

A ganina, dangatakar Sin da kasar Habasha, ba samar da hanyar bunkasa tattalin arziki kadai ta yi ba, har ma da samarwa kasar irin dabarar kasar Sin ta samun ci gaba. Mun sani cewa, kasar Sin ta bullo da wata sabuwar hanyar ci gaba da ba a taba gani ba a duniya, inda take juya yawan al’umma da albarkatun da take da su a cikin gida zuwa hanyoyin bunaksa ci gabanta ba tare da mulkin mallaka ba. Hakika hulda da kasar Sin alheri ce, kuma na yi imanin sauran kasashen Afrika za su iya bin sawun Habasha don tabbatar da ci gabansu.(Fa'iza Mustapha)