logo

HAUSA

Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar Da Rura Wutar Rikici Da Bata Sunan Wasu Sassa Dangane Da Batun Ukraine

2024-04-23 20:35:51 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na fatan Amurka za ta dakatar da rura wutar rikici, ko bata sunan wasu sassa don gane da batun Ukraine, domin hakan ba zai warware rikicin da kasar ke fama da shi ba.

Wang, ya yi tsokacin ne yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa na yau Talata, lokacin da yake amsa tambayoyi game da wasu rahotanni daga bangaren Amurka, masu kunshe da zargin alakar tattalin arziki da musaya tsakanin Sin da kasar Rasha. Game da hakan, Wang Wenbin ya ce, yayin da Amurka ke samar da tarin tallafi ga Ukraine, a daya bangaren ba gaira ba dalili, ta soki halastacciyar musayar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Rasha. Ya ce, “Yin hakan munafurci ne da rashin sanin ya kamata, kuma Sin na matukar adawa da hakan”.

Wang Wenbin ya kara da cewa, game da batun Ukraine, har kullum kasar Sin na nacewa matakai na gaskiya da adalci, tana kuma yayata bukatar rungumar matakan zaman lafiya da warware matsala ta hanyar siyasa. Kaza lika, Sin ba ta da hannu wajen kirkira, ko hannu cikin rikicin Ukraine. Bugu da kari, kasar Sin ba ta taba rura wutar rikicin, ko cin gajiya daga gare shi ba, kuma ba za ta amince a dora mata alhakin hakan ba.   (Saminu Alhassan)