logo

HAUSA

Sin Ta Yi Kira Ga Sassa Masu Ruwa Da Tsaki Da Su Dakatar Da Shiga Kulle-kullen Bata Sunan Kasar Sin

2024-04-23 20:46:32 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi tsokaci game da wasu rahotanni da suka fito daga kasashen Jamus da Birtaniya, game da zargin nan da wasu sassa ke yi wa kasar Sin, na “Barazanar Leken Asiri”. Yayin taron manema labarai na Talatar nan, Wang Wenbin ya ce, ko shakka babu, burin masu zarge-zargen shi ne bata sunan kasar Sin, da dakile kamfanonin kasar, da gurgunta yanayin hadin gwiwa tsakanin Sin da Turai. Kasar Sin na kira ga sassa masu ruwa da tsaki a wannan batu, da su kauracewa wannan manufa ta kulle-kullen siyasa na shafawa kasar Sin bakin fenti.

Kaza lika, Wang Wenbin ya ce, Sin na fatan dukkanin sassan za su yi watsi da tunani irin na lokacin cacar baka, su dakatar da fakewa da zargin “Barazanar Leken Asiri”, da nufin bata sunan kasar Sin.

Jami’in ya kara da cewa, karkashin manufarta ta martaba juna, da kin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, har kullum kasar Sin na yin hadin gwiwa da ragowar kasashen duniya bisa adalci, ciki har da kasashen Turai.  (Saminu Alhassan)