logo

HAUSA

Sin ta kalubalanci Amurka da ta dubi kanta game da yanayin kare hakkin dan Adam

2024-04-23 20:53:46 CMG Hausa

Game da rahoton da ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta gabatar don gane da batun kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, wanda ya zargi sauran kasashe da gazawa wajen kare hakkin dan Adam, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, rahoton na Amurka, ya zargi yanayin kare hakkin dan Adam na kasashe da yankuna kimanin 200 na duniya, amma bai ambato ita kanta Amurka ba. Don haka Sin ta kalubalanci Amurka, da ta dubi kanta, ta fara da warware matsalarta a wannan fanni.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, Amurka na gabatar da rahoton kare hakkin dan Adam na shekara-shekara, amma abubuwan dake shafar kasar Sin a rahoton jita-jita ne kawai domin kulle-kullen siyasa, matakin da Sin din ba za ta amince da shi ba.

Har ila yau, Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, idan Amurka na matukar mai da hankali ga kare hakkin dan Adam, to kamata ya yi ta daidaita matsalolin bindigogi, da miyagun kwayoyi, da nuna bambancin launin fata, da keta hakkin dan Adam dake faruwa a kasar, kana ta yi la’akari da matsalolin da ta kawo wa yankuna masu fama da rigingimu, ta hanyar tsoma baki, da samar da makamai, da kuma ta da zaune-tsaye. (Zainab Zhang)