logo

HAUSA

AU ta jajanta hatsarin kwale-kwale da ya auku a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

2024-04-22 10:53:29 CMG Hausa

Shugaban hukumar kungiyar Tarayyar Afrika (AU) Moussa Faki Mahamat, ya mika sakon jaje don gane da hatsarin kwale-kwalen da ya auku a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. Faki Mahamat ya wallafa sakon ne a shafin sada zumunta na X a ranar Asabar da dare, inda kuma ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su.

Hukumomi da mazauna yankin da lamarin ya auku, sun ce zuwa jiya Lahadi, adadin wadanda suka mutu sanadiyyar hatsrin da ya karu zuwa 62.

Hatsarin ya auku ne ranar Jumma’a, inda kwale-kwale dauke da mutane sama da 300 a kogin Mpoko dake Bangui babban birnin kasar, ya nutse.

Shaidun gani da ido sun ce fasinjojin na kan hanyarsu ne ta zuwa kauyen Mokelo, dake yankin Bimbo na gundumar Ombella-Mpoko, domin jana’izar wani shugabansu, a lokacin da lamarin ya auku. (Fa’iza Mustapha)