logo

HAUSA

Netanyahu: Isra’ila za ta kara matsawa Hamas lamba

2024-04-22 11:02:53 CMG Hausa

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya lashi takobin kara matsa kaimin matakan soji kan kungiyar Hamas.

Cikin jawabin da ya yi ta bidiyo a jiya Lahadi, Netanyahu ya yi barazanar daukar matakin cikin kwanaki masu zuwa, ba tare da bayyana lokaci da kuma wuri ba.

A cewarsa, cikin kwanaki masu zuwa, Isra’ila za ta kara matsawa Hamas lamba ta fuskar matakan soji da na diflomasiyya, saboda ita ce kadai hanyar sakin wadanda aka yi garkuwa da su, tare da cimma nasara.

A baya, Netanyahu ya bayyana cewa, sojojin Isra’ila za su fara kai farmkai ta kasa a Rafah, duk da kiraye-kirayen da kasa da kasa suka yi na kaucewa irin wannan mataki saboda mummunan tasirin da zai yi kan fararen hula sama da miliyan 1 dake neman mafaka a birnin dake kudancin Gaza. (Fa’iza Mustapha)