logo

HAUSA

Daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a Nijar don neman janye sojojin Amurka daga kasar

2024-04-22 15:41:34 CMG Hausa

Daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a birnin Agadez dake arewacin Jamhuriyar Nijar a jiya Lahadi, don neman janye sojojin Amurka dake kasar.

A ranar 19 ga wata, bisa rahotannin da wasu kafofin watsa labarai na Amurka suka fitar, bangaren Amurka ya amince da bukatar bangaren Nijar ta janye sojojin Amurka daga kasar. Wata majiya ta kuma bayyana cewa, bangarorin biyu za su tattauna kan jadawalin janye sojojin na Amurka a cikin wasu kwanaki nan gaba.

A halin yanzu, yawan sojojin Amurka dake Nijar ya kai kusan 1000, wadanda suke gudanar da harkokin sansanoni guda biyu.(Safiyah Ma)