Sin ba ta da masaniya game da dalilin Philippines na kin amincewa da daidaiton da aka cimma kan batun sashen tudun ruwa na Ren’aijiao
2024-04-22 20:17:19 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin da Philippines sun taba cimma daidaito, kan warware batun sashen tudun ruwa na Ren’aijiao, wanda hakan tabbataccen mataki ne na gaskiya, ba ma kawai a yayin mulkin gwamnatocin kasar Philippines na baya ba, har ma da na lokacin yanzu.
Wasu rahotanni na cewa, wani manazarcin harkokin tsaron kasar Philippines Eduardo Año, ya fitar da sanarwa a ranar 20 ga watan nan, wadda ke cewa gwamnatin Philippines ta yanzu, ba ta da masaniyar kowace yarjejeniya, ko sirri a tsakanin Philippines da Sin ba, kuma ko da ma gwamnatin kasar da ta gabata ta taba cimma yarjejeniya don gane da hakan, to a yanzu an soke ta.
Game da wannan batu, Wang Wenbin ya bayyana cewa, biyayya ga ra’ayi daya wanda Sin da Philippines suka cimma, zai tabbatar da halin da sashen tudun ruwa na Ren’aijiao zai kasance, tare da dacewa da moriyar kasashen biyu. Yayin da sabawa alkawarin zai tada zaune tsaye, da tsananta halin da ake ciki, har ma zai iya haifar da illa ga kasar Philippines ita kanta. A hannu guda kuwa, Sin na fatan Philippines za ta amince da gaskiya, tare da tsai da kuduri mai dacewa. (Zainab Zhang)