logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Amurka: Ana fatan Amurka da Sin su bi hanya daya don binciken yadda kulla abota tsakaninsu

2024-04-22 11:03:12 CMG Hausa

Jakadan Sin dake Amurka, Xie Feng, ya gabatar da jawabi a gun bude taron dandalin tattaunawa na Sin, na kwalejin gwamnatin John Fitzgerald Kennedy ta jami’ar Harvard a ranar 20 ga wata, inda ya bayyana cewa, ana fatan bangarorin Amurka da Sin za su bi hanya daya, bisa ka’idojin mutunta juna, da zaman jituwa, da kuma cimma nasara tare ta hanyar hadin gwiwa, da binciko madaidaicciyar hanya don kulla abota tsakaninsu a cikin sabon zamani.

Xie Feng ya bayyana cewa, duniya cike take da tangal-tangal. Hanyar da Sin ta zaba ba za ta sauya ba, wato inganta zamanintarwa irin na Sin, wanda shi ne babban tsarin ci gaban kasar, kuma gina al’umma mai makomar bai daya ta daukacin bil’adama, manufar Sin ce ta gina duniya mai kyau tare.

Xie Feng na fatan bangarorin Amurka da Sin za su yi kokari tare, su tsaya tsayin daka kan sauke nauyin dake wuyansu don kwantar da hankalin al’ummun kasashen biyu da na duniya, su kuma nuna kyakkyawar aniya wajen kulla dangantakar bangarorin biyu, da gudanar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma matsaya kansu, da ingnata mayar da “hangen nesa na San Francisco” zuwa “abu na zahiri”, ta yadda zai inganta ci gaban dangantakar Sin da Amurka a kan hanya mai kwanciyar hankali da zaman lafiya, kuma mai dorewa.

Wakilan masana a fannonin siyasa da kasuwanci na Sin da Amurka, da malamai da dalibai na jami’ar Harvard da kuma daliban Sin dake koyon ilmi a Amurka fiye da 300 sun halarci dandalin tattaunawar. (Safiyah Ma)