logo

HAUSA

Ya san abin da Sin take so da kuma wurin da za ta je

2024-04-22 07:05:53 CMG Hausa

Galina Kulikova, ita ce mataimakiyar shugaba ta farko ta kungiyar abota tsakanin Rasha da Sin. A shekarar 2019, ta sami lambar yabo mafi girma da jamhuriyyar jama’ar kasar Sin ke baiwa mutanen kasashen ketare, wato “lambar yabo ta abokantaka”.

Kulikova ta ce, “shugaba Xi Jinping ya dade tare da jama’ar kasar Sin, ya kuma dage wajen kafa tushensa cikin al’ummun kasar. Shugaba ne daidai da kasar Sin, shi da kasarsa dukkansu suna da kwanciyar hankali da kuma juriya. Ya san abin da Sin take so, kuma ya san inda kasarsa za ta nufi.” (Safiyah Ma)