logo

HAUSA

Ministocin sadarwa na kungiyar kasashen yankin Sahel AES sun ziyarci cibiyar data ta Nijar da ake ginawa

2024-04-22 11:01:23 CMG Hausa

A dab da makon internet, ministan sadarwan kasar Nijar Sidi Mohamed Raliou da takwarorinsa na Mali, Alhamdou Ag Ilyene, da ta kasar Burkina Faso, dokta Aminata Zerbo sun kai wata ziyarar gani da ido a ranar jiya Lahadi 21 ga wata.

Daga birnin Yamai, wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto

Ministocin uku na kasashen kungiyar AES sun ziyarci rumfunan baje koli na kamfanoni da ma’aikatun da ke aiki a fannin sadarwa a ranar Asabar 20 ga watan Afrilun shekarar 2024, kafin kuma ranar jiya su kai ziyarar gani da ido a katafaren wurin da ake gina cibiyar Data domin tattara da ajiyar bayanai a unguwar Lazaret da ke birnin Yamai.

Ayyukan gine ginen wannan babbar cibiyar Data domin tattara da ajiyar bayanai ta kasar Nijar, sun kai kashi goma cikin dari na ginawa.

Wata dama da ministan sadarwa na kasar Mali Alhamdou Ag Ilyene ya yi amfani da ita domin bayyana farin cikinsa na ganin kasashen Afrika sun himmatu musamman ma na kungiyar kasashen yankin Sahel na aiki domin tabbatar ‘yancin gashin kansu ta hanyar samun cibiyoyin Data na kansu. 

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.