logo

HAUSA

Kasar Sin na kokarin samar da ruwa ga yankunan dake fama da fari

2024-04-22 14:19:42 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin, ta ce ta matsa kaimi wajen samar da ruwa ga kimanin manya da matsakaitan yankuna 500 da ake ban ruwa, a yankuna masu fama da fari dake kudu maso yammacin kasar.

Zuwa yanzu, an kai jimillar cubic mita miliyan 160 na ruwa zuwa yankunan dake fama da fari, wadda ke samar da ruwa ga gonakin da jimillarsu ta kai sama da mu miliyan 3.5 ko kadada 230,000.

Baya ga haka, kasar Sin ta ware yuan miliyan 174 kimanin dala miliyan 24.49, domin inganta yaki da fari da tabbatar da wadatar ruwa. (Fa’iza Mustapha)