logo

HAUSA

An harba rokoki daga Iraqi zuwa sansanin sojan Amurka dake Syria

2024-04-22 10:00:43 CMG Hausa

Wata majiyar tsaro ta ce, an harba rokoki 5 daga Iraqi, zuwa wani sansanin sojin Amurka dake Syria a jiya Lahadi.

Majiyar daga rundunar ‘yan sandan lardin Nineveh na Iraqi wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wasu mayakan da ba a san ko su wane ne ba, sun harba rokokin daga wani kauye dake kusa da garin Zummar mai tazarar kilomita 60 da Mosul, babban birnin lardin Nineveh zuwa yankunan Syria.

Daga bisani wata sanarwa daga kafar yada labarai dake karkashin rundunar tsaron hadin gwiwa ta Iraqi, ta ce dakarun tsaron Iraqi sun kaddamar da farautar maharan a yammacin Mosul. Tana mai cewa, maharan sun harba rokokin ne da misalin karfe 9 da minti 50 na dare, wato karfe 1850 agogon GMT a jiya Lahadi.

Sanarwar ta kara da cewa, jami’an tsaron sun gano makamin harba rokokin a jikin wata mota tare da kona ta, yayin da suka ci gaba da farautar maharan da zummar cafke su domin su fuskanci hukunci. (Fa’iza Mustapha)