logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Gabon ya yabawa nasarorin da Gabon da Sin suka samu a fannonin sada zumunta da hadin gwiwa

2024-04-21 16:56:09 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Gabon Ali Akbar Onanga Y’obeghe ya yabawa nasarorin da kasashen Gabon da Sin suka samu a fannonin sada zumunta da yin hadin gwiwa a cikin shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu.

Onanga ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya yi a gun liyafar taya murnar cika shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Gabon da aka gudanar a birnin Libreville. Ya kuma bayyana cewa, a cikin rabin karni, an raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da fadada hadin gwiwarsu a dukkan fannoni, wanda ya amfanawa jama’ar kasashen biyu. A cewarsa, Gabon ta yi kokarin zurfafa dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, da nuna goyon bayan ka’idar “Sin daya tak a duniya”, kana tana son ci gaba da yin mu’amala tare da kasar Sin kan harkokin da suka shafi bangarorin biyu, da sa kaimi ga samun sabbin nasarori kan hadin gwiwarsu, da kuma tabbatar da adalci a duk duniya baki daya.

A nasa bangare, mukaddashin jakadan Sin dake Gabon Zhu Xiaole ya bayyana cewa, a cikin shekarun 50, Sin da Gabon sun kara imani da juna a fannin siyasa, da samun nasarori da dama kan hadin gwiwarsu, da kuma zurfafa yin mu’amala da juna a fannin al’adu. Ya ce a nan gaba, ya kamata bangarorin biyu su aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashensu suka cimma daidaito kansu, da raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu a dukkan fannoni, ta yadda za a raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka tare. (Zainab Zhang)