logo

HAUSA

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya: Yanzu darajar kudin kasar ya kai ga wani mahimmin matsayi

2024-04-21 16:22:21 CMG Hausa

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya ce yana da kyakkyawan yakinin cewa kudin kasar za su ci gaba da yin mummunan tasiri kan dalar Amurka a kasuwar musayar kudade ta duniya.

Ya bayyana hakan ne jiya Asabar lokacin da yake karbar bakuncin wakilan cibiyar kasuwanci da masana’antu ta jihar Lagos, karkashin jagorancin shugaban cibiyar Mr. Gabriel Idahosa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Sanata Kashim Shettima ya ce kawo karshen bayar da tallafin man fetur ya taimaka wajen tabbatar da daidaita farashin kudin canji zuwa na bai daya, wanda ya rusa tsohon tsarin da ake bi a baya wanda a wancan lokaci wasu tsiraru ke yin kudin cikin dare daya.

Ya ce baya ga farfado da darajar Naira, gwamnati kuma tana bakin kokarin ganin an shawo kan kalubalen da bangaren wutar lantarki ke fuskanta, wanda shi ma nan ba da jimawa ba komai zai daidaita.

“Wannan gwamnati karkashin jagorancin shugaba Tinubu ta himmatu sosai wajen kara fayyaci ma’ana da manufar jagoranci irin na zamani a aikace, saboda madogarar kowanne dan Afrika yana wuyan Najeriya ne.”

A jawabin sa, shugaban cibiyar kasuwanci da masana’antu ta jihar Lagos Mr. Idahosa bukatar gwamnatin Najeriya ya yi, kan ta tabbatar da inganta tsare-tsarenta na samar da rance ga ‘yan kasuwa da kyautata sha’anin zuba jari. (Garba Abdullahi Bagwai)