Zuwa 2033 Bangaren Aikin Gona Na Kasar Sin Zai Samu Ci Gaba Ta Kowace Fuska
2024-04-21 16:59:03 CMG Hausa
Cikin gomman shekaru masu zuwa, bangaren aikin gona na kasar Sin zai shaida ci gaba ta kowace fuska ta hanyar sabon karfin samar da ci gaba, wanda zai samu goyon baya daga karuwar sauye-sauye da kuma daukakar bangaren.
Wannan na kunshe ne cikin rahoton hasashen yanayin bangaren aikin gona na kasar Sin daga shekarar 2024 zuwa ta 2033, wanda aka fitar yayin taro kan hasashen bangaren aikin gona na kasar a bana, da ya gudana a kwalejin nazarin kimiyyar aikin gona ta kasar Sin.
A cewar rahoton, yawan hatsin da aka samar a shekarar 2023 ya kai ton miliyan 695, karuwar kaso 1.3 idan aka kwatanta da ta shekarar 2022. Kana aikin samar da hatsi a kasar a kowace shekara, ya kasance bisa yanayi mai daidaito, kan ton miliyan 650 cikin shekaru 9 jere.
An samu ci gaba sosai a fannin raya aikin gona mai inganci, inda aka samar da ingantattun gonaki da jimilarsu ta kai kimanin kadada miliyan 66.67 a fadin kasar, lamarin da ya kara bunkasa aikin samar da gonaki masu inganci.
Bisa la’akari da sabbin nasarori a fannin fasahar rainon kwayoyin halitta, da karuwar yabanya da tsare-tsaren fasahohi masu inganci da ci gaba da bunkasa ingancin gonaki, ana sa ran zuwa shekarar 2033, za a samu karuwar kaso 10.7 cikin dari na duk mizanin filin noma 1, wanda zai kai kilo giram 6,438 a kowace kadada 1. (Fa’iza Mustapha)