logo

HAUSA

Bloomberg: Sin za ta fi samar da gudummawa wajen raya tattalin arzikin duniya nan da shekaru 5 masu zuwa

2024-04-21 17:01:42 CMG Hausa

Kamfanin dillancin labaru na Bloomberg na kasar Amurka ya yi hasashen cewa, kasar Sin za ta fi samar da gudummawa wajen raya tattalin arzikin duniya nan da shekaru 5 masu zuwa, inda yawan gudummawar da za ta samar zai zarce adadin gudummawar dukkan kasashen kungiyar G7, kana zai ninka na kasar Amurka har sau biyu.

Bisa kididdigar da asunsun ba da lamuni na duniya wato IMF ya gabatar a wannan mako, kamfanin dillancin labaru na Bloomberg ya bayar da labarin cewa, tun daga shekarar 2024 zuwa ta 2029, kasar Sin za ta aiwatar da sabbin ayyukan tattalin arziki da kashi 21 cikin dari bisa na duk duniya, kuma yawansu da kungiyar G7 za ta samar zai kai kashi 20 cikin dari, kana na kasar Amurka zai kai kimanin kashi 12 cikin dari.

A takaice, kasashe 20 za su samar da kashi 75 cikin dari na bunkasuwar tattalin arzikin duniya nan da shekaru 5 masu zuwa, a cikinsu Sin, da Indiya, da Amurka, da Indonesia za su samar da gudummawar fiye da rabi. (Zainab Zhang)