logo

HAUSA

Falasdinu za ta sake nazarin dangantakarta da Amurka

2024-04-21 17:12:30 CMG Hausa

 

Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ya ce, shugabancin Palasdinu zai sake nazarin dangantakar dake tsakaninsa da kasar Amurka, bisa la’akari da matukar goyon bayan da take ba Isra’ila.

Mahmoud Abbas ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na WAFA, bayan Amurka ta hau kujerar naki don gane da daftarin kudurin dake neman Falasdinu ta zama cikakkiyar mamba a MDD.

Kamfanin dillancin labarai na WAFA ya ruwaito Mahmoud Abbas na sukar matakin na Amurka, yana mai bayyana shi a matsayin abun kunya da takaici da rashin sanin ya kamata, haka kuma mara dalili. Ya kara da cewa, matakin ya take hakkin Falasdinawa, kuma ya kalubalanci burin al’ummun duniya.

Ya kuma nanata cewa, za su sake nazarin dangantakarsu da Amurka domin tabbatar da kare muradunsu da na al’ummarsu da ma hakkokinsu.

Shugaban na Falasdinu ya jaddada cewa, shugabancin Falasdinu zai samar da wata sabuwar dabarar kare matakan da Falasdinu za ta dauka da kanta tare da bin ajandar da za ta samar, maimakon ra’ayin Amurka ko ajandun yanki. (Fa’iza Mustapha)