logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a dakatar da hare-haren ramuwar gayya tsakanin Iran da Isra’ila

2024-04-20 17:36:57 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a dakatar da hare-haren ramuwar gayya masu matukar hadari dake wakana a gabas ta tsakiya. Cikin wata sanarwa da kakaninsa Stephane Dujarric ya fitar, bayan bullar wasu rahotanni dake cewa Isra’ila ta kaddamar da hare hare ta sama kan wasu yankuna na kasar Iran, Guterres ya yi Allah wadai da hare hare tsakanin kasashen biyu, yana mai kira ga sassan kasa da kasa da su yi aiki tare, wajen dakile duk wani mataki daka iya kazanta halin da ake ciki a yankin, da ma sauran sassan kasa da kasa.

Sai kuma a ranar Juma’a sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce ba zai yi tsokaci kan rahotannin kafofin watsa labarai ba, dangane da ainihin yadda ya wakana, a harin tsakar dare da Isra’ila ta kaiwa Iran ba, yana mai cewa Amurka ba ta da hannu cikin wannan mataki na gwamnatin Isra’ila.

A wata sabuwa kuma, cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, kungiyar fafutuka ta Islama dake Iraqi, ta ce ta kaddamar da harin jirgi maras matuki kan yankin Eilat na Isra’ila, ‘yan sa’o’i bayan da wasu jirage marasa matuki suka tarwatsa wani sansanin soji na dakarun Hashd Shaabi dake tsakiyar kasar Iraqi.