logo

HAUSA

Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce ba za ta taba saurarawa kowacce kungiya ko wani mutum da ya dauki makami da niyyar neman ‘yancin wani yanki a kasar ba

2024-04-20 19:36:08 CMG Hausa

Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi kurarin cewa za ta zartar da hukunci mai tsananin gaske kan duk wata kungiya ko wani mutum da ya dauki makami da nufin fafutukar neman raba kasa ko wani yanki daga Najeriya.

Daraktan harkokin yada labarai na hedkwatar tsaron Major Janaral Adward Buba ne ya yi wannan gargadi ranar Alhamis yayin taron manema labarai na mako-mako da ya saba gudanarwa a birnin Abuja .

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Manjo Janar Edward Buba ya bayyana takaicin kan yadda wasu marasa kishin kasa suka tada hankalin al`umma da zummar neman a raba yankin Yarbawa dake kudu maso yammacin Najeriya, lamarin da ya bayyana da cewa tsantsar son zuciya ne kawai da neman yi wa dokar kasa karan tsaye.

Ya ce ko kadan hedkwatar tsaro ta kasa ba za ta zuba ido irin wannan halayya ta ci gaba da wakana ba a kowanne sashe na Najeriya, domin kuwa kamar yadda ya fada Najeriya kasa ce mai `yanci wadda take kuma a dunkule.

Daraktan yada labaran na rundunar tsaron ta Najeriya ya ce an samu nasarar kame gungun mutanen da suka yi yunkurin tada zaune tsaye a jihar ta Oyo, kuma tuni rundunar tsaron ta kasa ta samu bayanan dake nuna cewa akwai masu kokarin bata sunan rundunar sojin Najeriya saboda nasarorin da take ta samu bayan farmaki ta sama da ake kan yi zuwa maboyar `yan ta`adda.

“Abun da ya faru a garin Ibadan inda wasu mutane sanye da kayan kakin soja suka yi yunkurin karbe majalissar dokokin jihar ta hanyar daga wata tuta ta daban babban laifi ne mutuka”

Yanzu haka dai masu neman tada da zaune tsayen da adadin su ya kai 24 wanda kuma suka kunshi mata 5, kotun majistare ta jihar Oyo ta  tuhume su da laifuka guda 7 da suka hada da cin amanar kasa da kirkirar haramtaciyar kungiya da mallakar makamai ba bisa izini ba, wanda kuma tuni ta aike da su gidan gyaran hali.(Garba Abdullahi Bagwai)