Yankin kudancin tekun Pasifik ba zai zamo dandalin hamayyar kasashe masu karfi ba, in ji ministan wajen Sin
2024-04-20 21:41:29 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce yankin kudancin tekun Pasifik, ba zai zamo dandalin hamayyar manyan kasashe masu karfin fada a ji ba.
Wang ya bayyana hakan ne a Asabar din nan, yayin taron manema labarai da ya gudanar tare da takwaran aikinsa na Papua New Guinea Justin Tkatchenko lokacin da ya ziyarci kasar. Ya ce ba wata kasa dake da ikon mayar da wata kasar dake yankin fagen da za ta iya yin duk abun da take so.
A wani ci gaban kuma, Wang Yi ya ce gaggauta amincewa da bukatar Falasdinu ta zama mamba a MDD, mataki ne da zai gyara rashin adalci na tsawon lokaci da aka tafka a tarihi. (Saminu Alhassan)