logo

HAUSA

Kasar Amurka na illata al’amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya

2024-04-20 21:37:34 CMG Hausa

'Yan siyasar Amurka da ke cewa suna goyon bayan 'shirin kafa kasashe biyu' ba sa goyon bayan kafa kasar Falasdinu.” "Abin da ake kira 'kasa mafi girma a dimokuradiyya' babbar karya ce." …A cikin 'yan kwanakin nan dai ana ci gaba da suka a shafukan sada zumunta na kasashen ketare, dangane da matakin da kasar Amurka ta dauka na kin amincewa da bukatar Falasdinu ta zama mamba a Majalisar Dinkin Duniya.

Kasashe da dama kamar Sin, da Masar, da Ireland da dai sauransu, sun nuna rashin jin dadinsu kan hakan. Kwamitin hadin gwiwa na kasashen yankin Gulf ya fitar da wata sanarwa, inda ya soki matakin da Amurka ta dauka na ja da baya, a kokarin da ake na ganin an samar da zaman lafiya mai cike da adalci a yankin gabas ta tsakiya.

A matsayinta na mamba ta dindindin a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, Amurka ta kada kuri'ar kin amincewa a ranar 18 ga wata bisa agogon wurin, ba tare da jin kai ba, inda ta wargaza mafarkin al'ummar Palasdinu na tsawon shekaru fiye da goma. Wannan ya sake fallasa munafuncinta da "ma'auni biyu" da take dauka kan batun Isra'ila na Falasdinu.

Wani abin zambo shi ne, Linda Thomas Greenfield, wakiliyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, ta yi ikirarin cewa shigar Falasdinu a hukumance cikin majalisar ba zai taimaka wajen cimma matsaya kan “shirin kafa kasashe biyu” na warware rikicin Falasdinu da Isra'ila ba. Abun tambaya ga wannan wakiliya ta Amurka shi ne, mene ne zai taimaka wajen cimma "shirin kafa kasashe biyu"? Shin makaman da Amurka ta aikewa Isra'ila akai-akai ne za su taimaka? Ko kuwa kuri'un adawa da ta jefa daya bayan daya a Majalisar Dinkin Duniya? Wadannan ayyukan da suka kauce wa zaman lafiya sun kara tabbatar da cewa, Amurka mai ruguza al'amuran kasa da kasa da shiyya-shiyya ce. Kuma babu wanda ke da ikon jefa kuri’ar ta-ki kan batutuwan da suka shafi makomar al'ummar Palasdinu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)