logo

HAUSA

Ofishin MDD da na jakadancin Sin a Kenya sun gudanar da bikin ranar harshen Sinanci ta MDD

2024-04-20 17:41:58 CMG Hausa

A jiya Juma’a ne ofishin MDD dake birnin Nairobin kasar Kenya, da na jakadancin Sin dake kasar, suka gudanar da bikin ranar harshen Sinanci ta MDD, ta hanyar shirya kasaitaccen biki.

Jakadan Sin a Kenya Zhou Pingjian, da babbar darakta a ofishin MDD dake Kenya Zainab Hawa Bangura na cikin mahalarta bikin. Manyan jami’an biyu sun jaddada muhimmancin ranar harshen Sinanci ta MDD, wadda a bana ta fado yau Asabar 20 ga watan nan na Afirilu, bisa yadda take ba da damar yayata cudanyar sassa daban daban, da samar da makomar bai daya ga dukkanin bil adama.

Cikin jawabinta na bude taron, uwargida Bangura, ta ce a matsayinsa na harshe da kaso daya bisa biyar na daukacin al’ummar duniya ke magana da shi, harshen Sinanci na taka muhimmiyar rawa wajen ingiza cudanyar sassa daban daban, da kuma fadada cudanyar al’adu.

Bangura ta ce harshen Sinanci na daya daga cikin harsunan MDD a hukumance. An kuma fara bikin ranarsa a shekarar 2010, wanda hakan ya taimaka matuka wajen zurfafa fahimtar sassan duniya game da al’adun kasar Sin.

Yayin bikin ranar, wanda ya gudana a ofishin MDD dake birnin Nairobi, an yi ayyuka daban daban, ciki har da rubuce-rubucen zayyana, da lakcoci, da kade-kade na rukunin makada daga jami’ar Nanjing, wadda daya ce daga manyan jami’o’in dake nahiyar Asiya.  (Saminu Alhassan)