logo

HAUSA

Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito cewa cikin 'yan watanni masu zuwa Amurka za ta janye kusan sojoji 1,000 daga Nijar

2024-04-20 16:57:35 CMG Hausa

A jiya Jumma’a 19 ga watan nan, wasu kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun labarta cewa, Amurka za ta kwashe kusan jami’an sojoji 1,000 daga Jamhuriyar Nijar a cikin watanni masu zuwa.

A cewar rahotanni da dama daga kafafen yada labarai na Amurka, irinsu The New York Times, mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Kurt Campbell, ya gana da firaministan gwamnatin rikon kwaryar Nijar Lamine Zeine a birnin Washington, fadar mulkin Amurka a jiya Jumma’a, inda Amurkan ta amince da bukatar Nijar na kwashe sojojinta daga kasar.

A cewar wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Amurka, sassan biyu za su fara tattaunawa a cikin kwanaki masu zuwa, dangane da jadawalin janyewar sojojin na Amurka.

A halin yanzu dai, akwai sojojin Amurka kimanin 1,000 a Nijar, wadanda ke aiki a sansanoni guda biyu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)