Wani jami’an Amurka ya tabbatar da harin makamai masu linzami da Isra’ila ta kaddamar a yankin kasar Iran
2024-04-19 13:44:18 CMG Hausa
Wani jami’in kasar Amurka ya shaidawa kafar watsa labarai ta ABC cewa, wasu makamai masu linzami da Isra’ila ta harba a jiya Alhamis, sun sauka cikin kasar Iran, ko da yake jami’in bai tabbatar da ko hare haren sun shafi yankunan Syria da Iraki ba.
A nasa bangare, kamfanin dillancin labarai na Iran, ya bayyana a yau Juma’a cewa, an jiyo karar wasu ababen fashewa a kusa da filin jiragen sama na Isfahan, da sansanin jiragen sama na Shekari.
Har ila yau, ita ma kafar talabijin ta Al Jazeera ta bayar da labari a Juma’ar nan cewa, sashen lura da sufurin jiragen sama na kasar Iran, ya sanar da dakatar da zirga zirgar jiragen sama daga filayen jiragen sama na Tehran da Isfahan na wani dan lokaci.
Bugu da kari, a dai yau Juma’a, kafar kamfanin dillancin labaran Iran, ta ce Iran ta kunna tsarin na’urorinta na tsaron sama, a sassa da dama na lardunan kasar. (Saminu Alhassan)