logo

HAUSA

Sin na tsayawa kan goyon bayan Falasdinu don zama mamba a hukumance a MDD

2024-04-19 21:37:44 CMG Hausa

Jiya Alhamis, 18 ga wata, kasar Amurka ta yi watsi da daftarin kuduri a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya game da bukatar da Falasdinu ta gabatar game da zama mamba a hukumance a majalisar. Game da wannan batun, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana cewa, a ko da yaushe kasarsa na tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya, da adalci, da kuma lamiri kan batun Palasdinu. A cewarsa, Sin na tsayawa kan goyon bayan Falasdinu don zama mamba a hukumance a MDD, za kuma ta ci gaba da yin aiki tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa don yin kokari da kuma taka rawar gani wajen kawo karshen rikici a zirin Gaza tun da wuri, da sassauta yanayin jin kai, da ma inganta aiwatar da "shirin kasashe biyu".

Haka zalika, game da boma-bomai da aka tayar a tsakiyar kasar Iran, wanda a cewar jami’an kasar Amurka ga kafofin watsa labaru, kasar Isra’ila ce ta kai wannan harin, kakakin ya bayyana cewa, kasar Sin ta lura da labaru masu nasaba da haka, tana kuma adawa da duk matakan da za su illata tsananin halin da ake ciki a yankin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)