Amurka ta hau kujerar na ki game da bukatar Falasdinu ta zama cikakkiyar mamba a MDD
2024-04-19 11:11:49 CMG Hausa
Kasar Amurka ta hau kujerar na ki, game da bukatar Falasdinu ta neman kasancewa cikakkiyar mamba a MDD, bukatar da aka gabatar yayin zaman kwamitin tsaron majalissar na jiya Alhamis.
An dai kada kuri’u kan kudurin da aka gabatar wa MDD mai mambobi 193, na neman mayar da falasdinu cikakkiyar mamba a majalissar. Kudurin ya samu kuri’un amincewa 12, kana mambobi 2 sun ki jefa kuri’unsu, yayin da kuma Amurka ta kada kuri’ar rashin amincewa da shi.
Bisa doka, kafin kudurin ya samu amincewa, wajibi ne ya samu kuri’un goyon bayan a kalla guda 9, kana kada daya daga cikin kasashe masu kujerar na ki, wato Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Rasha da Sin ta bayyana adawa da bukatar. Hakan ne kuma ya sanya Amurka ta hau kujerar na ki kan kudurin, domin hana samun nasarar sa, bayan da kudurin ya samu kuri’un amincewa 12.
Kafin hakan, cikin farkon watan nan, kwamitin MD mai lura da bukatar kara sabbin mambobi, ya nazarci bukatar da Falasdinawa suka mika, na samun amincewar zama cikakkiyar mamba, kudurin da ya samu amincewar kasashe 140, masu daukar Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kai. (Saminu Alhassan)