Wakilin kasar Sin ya bukaci goyon baya ga bukatar Falasdinawa ta samun ‘yancin kai
2024-04-19 11:21:57 CMG Hausa
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su kauracewa watsi da dadaddiyar bukatar nan ta Falasdinawa, ta neman ‘yancin kai da kafuwar kasar su, kana kada a wanzar da rashin adalcin da al’ummar Falasdinu ta jima tana fuskanta.
Yayin mahawarar manyan jami’an kwamitin tsaron MDD da aka gudanar game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila a jiya Alhamis, Fu ya tabo batu kan muhimmiyar bukatar maida hankali matuka ga tabbatar da nasarar kafuwar kasashe biyu masu cin gashin kai.
Fu ya kara da cewa, ya zama wajibi a sa kaimi ga cimma nasarar kafuwar kasashen biyu. Kaza lika, ginshikin warware kalubalen dake addabar gabas ta tsakiya shi ne kafa kasashe biyu masu ‘yanci, ta yadda Falasdinawa da al’ummar Isra’ila za su cimma nasarar samun tsaro na bai daya, a hannu guda kuma, bangarorin Larabawa da na Yahudawa za su cimma nasarar ci gaban bai daya. (Saminu Alhassan)