logo

HAUSA

An fara gudanar da babban taron shekara lura da harkokin tsaron ruwa na kasashen dake gabar tekun Guinea

2024-04-19 09:11:38 CMG Hausa

Hukumar gudanarwar kungiyar Ecowas ta bayyana gamsuwa bisa namijin kokarin cibiyar kasa da kasa dake lura da sha’anin tsaro a bangaren sufurin jiragen ruwa a gabar tekun Guinea.

Shugaban hukumar Dr. Omar Touray ne ya yi yabon a birnin Abuja ranar Alhamis 18 yayin babban taro karo na 4 na shugabannin hukumomin lura da sufurin jiragen ruwa na kasashen Afrika da suke hada-hada a gabar tekun Guinea.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Kungiyar Ecowas da kungiyar kasashen dake tsakiyar Afrika da kuma hukumar dake lura da gabar tekun Guinea ne suka kirkiri ita wannan cibiya a cikin watan Satumbar 2014 bayan taron da shugabannin kasashen suka gudanar a Yaounde ta kasar Kamaru, kuma an samar da ita ne hususan domin samar da kariyar tsaro ga jiragen ruwan dake sintiri a gabar tekun.

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta Ecowas ya ce, an samu ci gaba sosai a bangaren sufurin jiragen ruwa a tsakanin kasashen dake nahiyar ta Afrika tun bayan samar da ita wannan cibiya.

Ya alakanta wadannan nasarori bisa kulla yarjejeniya da aka yi da wasu manyan kasashen duniya wadanda suke baiwa cibiyar kudade baya ga kudaden da gwamnatoci ke ware mata a duk shekara.

Dr. Omar Toury ha’ila yau ya ce, samu da ganin muhimmancin cibiyar ne wajen tabbatar da tsaro a harkokin sufurin jiragen ruwa a duniya baki daya, ya sanya wasu kasashen duniya nuna sha’awar yin aiki tare da cibiyar.

“Muna matukar godiya ga kungiyar tarayyar Turai da gwamnatin kasar Jamus da kuma gwamnatin kasar China saboda goyon baya da taimako daban daban da suke baiwa cibiyar.”

Ya tabbatar da cewa, a yanzu haka yankin gabar tekun na Guinea yana ci gaba da samun saukin ayyukan ’yan fashin teku da sauran hare-haren barayi. (Garba Abdullahi Bagwai)