logo

HAUSA

Jakadan Sin a MDD ya soki lamirin kin amincewa da bukatar Falasdinu ta zama mamba a MDD

2024-04-19 15:44:24 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya yi matukar sukar kasashen da suka aza ayar tambaya game da bukatar Falasdinu, ta zama mamba a MDD karkashin tanadin kudurin majalissar mai nasaba da hakan. Yana mai cewa bukatar halastaccen hakki ne na al’ummar Falasdinawa.

Cikin sanarwar da ya fitar bayan kada kuri’a game da kudurin, wanda Amurka ta ki amincewa da shi, Fu Cong ya bayyana matukar baikensa ga hakan. Jami’in ya kuma yi kira da a baiwa Falasdinu cikakken matsayin mamba a MDD a matsayin matakin daidaita ta da Isra’ila, wanda hakan zai samar da cikakken kyakkyawan yanayin komawa shawarwari.

Daga nan sai Fu ya jaddada matsayar kasar Sin ta ci gaba da kokari, da taka rawar gani wajen tabbatar da wannan manufa, tare da fatan a nan gaba al’ummun Falasdinu da na Isra’ila za su iya rayuwa tare cikin walwala da farin ciki.   (Saminu Alhassan)