logo

HAUSA

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Neman Zama Madaukakiya Tare Da Sake Waiwayar Dokokin Kasa Da Kasa

2024-04-18 15:01:00 CMG Hausa

 

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi fatan Amurka za ta dakatar da yunkurin da take yi na neman zama madaukakiya, kana ta natsu wajen sauraren muryoyin sassan kasa da kasa.

Wang Yi, wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin taron hadin gwiwa na ganawa da ‘yan jaridu, bayan zantawa da takwararsa ta kasar Indonesia Retno Marsudi.

Ya ce, ya kamata jami’an kasar Amurka su yi nazari a fannin ilimin dokokin kasa da kasa tabbatattu. Wang ya ce, kasar Sin a shirye take ta ci gaba da aiki tare da sauran kasashe mambobin kungiyar yankin kudu maso gabashin Asiya, a fannin aiwatar da yarjejeniyar gudanar da cudanya a tekun kudancin Sin, da ingiza tattaunawa game da tsare-tsaren aiwatar da harkoki a yankin tekun kudancin Sin, ta yadda za a gina shi ya zama mai yanayin zaman lafiya da hadin gwiwa.  (Saminu Alhassan)