logo

HAUSA

Wakilin Sin A MDD Ya Yi Kira Da A Ceto Rayuwar Matasan Gaza

2024-04-18 11:10:22 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya jaddada muhimmancin shawo kan mawuyacin hali da matasan zirin Gaza ke ciki.

Fu Cong, wanda ya yi tsokacin a jiya Laraba, yayin mauhawarar kwamitin tsaron MDD, game da rawar da matasa za su iya takawa wajen shawo kan kalubalen tsaro a yankunan tekun Bahar Rum, ya ce daya daga ginshikan kafa MDD shi ne ceton al’ummu na gaba daga mummunan tasirin yaki.

Jami’in ya kuma yi bitar irin illar da tashin hankali a Gaza ya haifar, yana mai cewa, bayan shafe sama da watanni 6, yakin ya hallaka sama da mutane 34,000. Ciki har da matasa da dama da baraguzan gine-gine suka binne, suna juyayin mutuwar ‘yan uwan da suka rasa.

Fu ya kuma yi kira da a dakatar da bude wuta nan take, a kuma janye shingaye domin bayar da damar shigar da tallafin jin kai, yana mai cewa, abu ne mai matukar muhimmanci a aiwatar da kudurin kwamitin tsaron MDD mai lamba 2728, da cimma nasarar tsagaita wuta nan take.

Daga nan sai jami’in ya jaddada wajibcin janye shingaye a zirin Gaza, ta yadda za a iya fadada damar shigar da tallafin jin kai, da samarwa mazauna yankin ababen bukata na wanzar da rayuwa.  (Saminu Alhassan)