logo

HAUSA

An gudanar da taron gabatar da CIIE karo na bakwai a kasar Zimbabwe

2024-04-18 11:25:25 CMG Hausa

Hukumar kula da harkokin baje kolin kasa da kasa, ta kayayyakin da ake shigarwa kasar Sin ko CIIE, da ofishin jakadancin Sin dake Zimbabwe, da hukumar inganta cinikayyar Zimbabwe da sauransu, sun gudanar da taron gabatar da baje kolin CIIE karo na bakwai a birnin Harare, fadar mulkin kasar, inda ma’aikatan gwamnati, da wakilan ’yan kasuwa na Zimbabwe suka halarci bikin.

Zaunanniyar sakatariyar dindindin ta ma’aikatar harkokin waje da cinikayyar kasa da kasa ta Zimbabwe Rofina Chikava, ta bayyana cikin jawabinta cewa, taron gabatarwar na wannan karo zai taimaka wajen inganta cinikayyar bangarorin biyu, wato Zimbabwe da Sin, kuma zai inganta hadin gwiwar tattalin arziki, da cinikayya tsakanin kasashe da yankunan duniya.

A nasa bangare kuwa, jakadan Sin dake Zimbabwe Zhou Ding ya bayyana cewa, bisa zurfafa dangantakar bangarorin biyu, cinikayya tsakanin Sin da Zimbabwe ta ci gaba da karuwa a shekarun baya bayan nan. Alkaluma sun bayyana cewa, a shekarar 2023, yawan kudaden cinikayyar bangarorin biyu ya kai dalar Amurka biliyan 3.122, wanda ya karu da kaso 29 cikin dari, idan an kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar 2022. Kaza lika dandali irin su CIIE, sun zama muhimman tagogi na nuna kayayyaki na musamman na Zimbabwe.

Bugu da kari, an fahimci cewa, kamfanoni 15 na Zimbabwe da suka shafi sarrafa fata, da sarrafa abinci, da zane-zanen fasaha, da fasahar sadarwa, da hakar ma'adanai, da makamashi, da yawon shakatawa da sauransu, sun shiga CIIE karo na shida da aka shirya a bara, kuma an yi hasashen cewa, yawan kamfaonin Zimbabwe da za su halarci CIIE na bana zai zarce hakan. (Safiyah Ma)