logo

HAUSA

Za a baiwa manoma horo na musamman tare da kayan aikin gona na zamani domin bunkasa sana’ar noman abinci a Najeriya

2024-04-18 14:29:08 CMG Hausa

Ma’aikatar gona ta tarayyar Najeriya ta nanata kudurin gwamnati wajen bunkasa kwazon manoma da samar musu da kayayyakin aiki na zamani domin kaiwa ga burin da ake da shi a duniya ta fuskar wadatuwar abinci mai gina jiki.

Ministan ma’aikatar Sanata Abubakar Kyari ne ya tabbatar da hakan jiya Laraba a wajen bikin baje kolin fasahar kayan amfanin gona na musamman da yake ci gaba da wakana a birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.  ///

 

Taken bikin baje kolin na bana dai shi ne dorewa da kuma kyautata harkokin samar da abinci ta amfani da sabbin fasahohi, inda ya kara da cewa, yanzu lokaci ya wuce da za a rinka amfani da tsohuwar hanyar dabarun aikin noma a Najeriya.

Ministan wanda ya sami wakilcin daraktan harkokin kasuwanci na ma’aikatar Mr. Gagare Nadono ya ce, akwai miliyoyin manoma ’yan Najeriya da suke bayar da gudummawarsu ga ci gaban tattalin arzikin cikin gida, to amma kuma suna cin karo da kalubale da dama, kama daga karancin albarkatu, asarar amfani bayan girbi da rashin samun kwarewar noman zamani da kuma karancin kayayyakin aikin gona, a saboda haka yanzu gwamnati za ta yiwo odar kayan aikin gona na zamani domin rabawa ga kananan manoman kasar.

“Kokarin da gwamanti take yi wajen inganta aikin noma bai tsaya kawai ga kokarin amfani da sabbin kayayyakin fasaha ba kadai, ya hada da ilimintar da manoma a kan sabbin dabarun noma da samar musu da kayan aiki da suke bukata domin samun nasara  sana’arsu na samar da  abinci a kasuwannin a duniya.”(Garba Abdullahi Bagwai)