logo

HAUSA

IMF ya daga hasashen bunkasar tattalin arzikin duniya na bana zuwa kaso 3.2

2024-04-17 11:19:20 CMG Hausa

Asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya daga hasashensa na bunkasar tattalin arzikin duniya na shekarar nan ta 2024 zuwa kaso 3.2, wanda ya nuna karuwar kaso 0.1 bisa dari kan hasashen da ya yi a watan Janairun da ya gabata.

Sabon hasashen dai na kunshe cikin rahoton nazarin yanayin tattalin arzikin duniya ko WEO, wanda IMF din ya fitar a jiya Talata, wanda kuma ya bayyana cewa duk da rashin kyawun hasashen sosai, tattalin arzikin duniya na nuna matukar yanayin juriya, mai kunshe da madaidaicin ci gaba, da hauhawar farashi mai sauka cikin sauri kamar yadda ya kan daga a baya.

Yayin zantawa da ’yan jaridu a taron jami’an IMF da bankin duniya na bazarar shekarar nan ta 2024, babban masanin tattalin arziki na IMF, kuma daraktan sashen binciken asusun Pierre-Olivier Gourinchas, ya ce akasarin alamu na nuna yiwuwar samun saukin al’amuran tattalin arzikin duniya a nan gaba.

IMF ya yi hasashen cewa, kasashe dake kan gaba wajen bunkasar tattalin arzikin duniya za su samu ci gaban kaso 1.7 bisa dari a shekarar nan ta 2024, karuwar da ta kai ta kaso 0.2 bisa dari kan ta watan Janairu. Kaza lika tattalin arzikin Amurka zai karu da kaso 2.7 bisa dari a 2024, zai kuma ragu zuwa kaso 1.9 bisa dari a shekarar 2025.

Har ila yau, tattalin arzikin Turai zai karu da kaso 0.8 bisa dari a shekarar nan ta 2024, karuwar da za ta kai kaso 1.5 bisa dari ya zuwa shekarar 2025.

Bugu da kari, IMF na hasashen tattalin arzikin kasashe masu samun saurin bunkasuwar tattalin arziki, da mafiya ci gaba, zai karu da kaso 4.2 bisa dari a 2024, karuwar da za ta kai ta kaso 0.1 bisa dari daga hasashen da asusun ya yi a watan Janairun da ya shude. IMF ya kuma yi hasashen cewa, tattalin arzikin Sin zai karu da kaso 4.6 bisa dari a shekarar 2024.   (Saminu Alhassan)