logo

HAUSA

Tawagar nazarin hada hadar kudade ta Sin da Amurka ta gudanar da taro karo na hudu a Washington

2024-04-17 13:59:29 CMG Hausa

Tawagar nazarin hada hadar kudade ta Sin da Amurka, ta gudanar da taro karo na hudu a jiya Talata a birnin Washington na Amurka. Yayin taron wakilan sassan biyu sun gudanar da tattaunawar kwararru, da musaya mai ma’ana bisa sahihanci, game da manufofin kudi na kasashen biyu, da daidaiton hada hadar kudade, da hadin gwiwa a fannin kiyaye ka’idojin hada hadar kudi, da sauran batutuwa masu jawo hankulan su, kamar dai yadda babban bankin kasar Sin ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar a Larabar nan.

Sanarwar ta ce taron ya gudana ne karkashin jagorancin mataimakin gwamnan babban bankin kasar Sin Xuan Changneng, da mataimakin sakataren sashen lura da harkokin kudi na kasa da kasa na baitil-malin Amurka mista Brent Neiman. (Saminu Alhassan)