logo

HAUSA

Shugaban Iran: za a mayar da martani ga duk wani mataki na kara illata moriyar Iran

2024-04-17 10:52:26 CMG Hausa

Fadar shugaban kasar Iran ta bayar da sanarwa a jiya Talata, cewa shugaban kasar Seyed Ebrahim Raisi, ya zanta ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Kuma yayin tattaunawar shugaba Raisi ya ce za a mayar da martani mai karfi ga duk wani mataki da zai illata moriyar Iran.

Shugaba Raisi ya bayyana cewa, harin da kasar Isra’ila ta kaiwa tawagar diplomasiyyar Iran ya sabawa ka’idojin kasa da kasa, ciki har da “Yarjejeniyar Raya Dangantakar Diplomasiyya Ta Vienna”. Kuma kasar Iran ta mayar da martani bisa ka’ida ta 51 ta “Kundin Tsarin Mulkin MDD”, wanda mataki ne na kare kanta. (Zainab)