An yi bikin Ranar Sinanci ta 2024 a hedikwatar UNESCO
2024-04-17 21:58:40 CMG Hausa
An kaddamar da bikin murnar Ranar Harshen Sinanci ta Majalisar Dinkin Duniya ta shekara ta 2024 na tsawon kwanaki biyar a shekaranjiya, 15 ga wata, a hedikwatar hukumar UNESCO dake birnin Paris na kasar Faransa.
Taken bikin na bana shi ne, harshen Sinanci, ya kafa gadar mu’amalar wayewar kai. Mataimakin babban darektan hukumar UNESCO, Qu Xing ya bayyana a wajen bikin cewa, harshe na tattare da al’adu iri-iri, kuma UNESCO ta kan bada shawarar raya mabambantan harsuna gami da al’adu. A halin yanzu, ana kara samun matasan kasar Faransa dake karatun harshen Sinanci, al’amarin dake da alaka sosai da ci gaban kasar Sin cikin sauri.
Harshen Sinanci, na daya daga cikin manyan harsunan aiki guda shida na MDD, kana, daya daga cikin harsunan dake samun masu amfani da su mafi yawa a duniya. (Murtala Zhang)