logo

HAUSA

Kafofin yada labaru na gwamnati da masu zaman kansu sun kafa wata hadaka da ake kira “CAP-MEDIAS-NIGER”

2024-04-17 09:41:22 CMG Hausa

A ranar jiya Talata 16 ga watan Afrilun shekarar 2024, kungiyoyin ’yan jarida na gwamnati da masu zaman kansu suka kafa wani kawance da ake kira tsarin shawarwari na kafofin watsa labarai na kasar Nijar CAP-MEDIAS-NIGER. Taron kafa wannan hadaka ya gudana a dakin taro na kungiyar Rotab da ke birnin Yamai.

Daga birnin Yamai, din abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

’Yan jarida, da masu kula da na’ura da masu gabatar da shirye-shirye da makamantansu na gwamnati da masu zaman kansu, sun dauki niyyar kafa wannan kawance na Cap-Medias-Nijar.

Mahalarta taron sun kafa wannan kawance bayan shawarwari tsakanin bangarorin biyu kan makomar aikin jarida a Nijar, da kuma yadda kwararrun ’yan jarida maza da mata za su kara nacewa wajen tafiyar da aikinsu na ilimantarwa, fadakarwa da nishadantarwa, da kuma kyautata ’yan cin fadin albarkacin baki cikin wannan lokaci na sake dora kasar Nijar bisa sabuwar alkibla cikin yanayin kishin kasa da ceton kasa.

A cewar shugabannin kawancen Cap-Medias-Niger, shi ne na kare muradun ma’aikatansu, da kuma kasancewa masu shiga tsakani wajen warware matsalolin dake iyar tasowa, da kuma neman hanyoyin kara kyautata jin dadin ma’aikatan kafofin sadarwa na gwamnati da masu zaman kansu.

Kawancen na Cap-Medias-Niger ya dauki alkawalin mai da hankali wajen horar da mambobinsa kan sanin makamar, sanin dokoki da sharudan aikin jarida, domin ganin ’yan jarida sun zama masu tantance da neman sahihancen labari ta yadda labarin da za su baiwa al’umma ya kasance labari mai taimakawa ga ci gaban kasa da zaman lafiya.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.