Abu Mafi Muhimmanci A Yanzu Shi ne Tsagaita Bude Wuta Da Kuma Kawo Karshen Rikicin Gaza
2024-04-17 08:03:38 CMG Hausa
Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji sun ce Gaza na fama da matsanancin karancin abinci da sauran muhimman abubuwa da suka hada da man fetur da magunguna. Wannan lamari dai ya fi kamari a arewacin Gaza, inda da wuya ake samun damar kai kayan agaji zuwa cikin yankin, yayin da hukumomin jin kai da Isra'ila ke ci gaba da zargin juna. Hukumomin jin kai sun ce binciken da jami'an tsaron Isra'ila ke yi kan kayan agajin da ke shiga Gaza na da sarkakiya kuma ba bisa ka'ida ba, wanda ke haifar da tsaiko. Ita kuma Isra'ila ta musanta cewa tana hana a kai agajin, ta kuma ce hukumomin ne suka gaza aiwatar da aikinsu yadda ya kamata. Duk da mawuyacin hali da ake ciki, Isra’ila na ci gaba da fatattakar Gaza da bama-bamai wanda ke rutsawa da jami’an agaji, misalin baya-bayan nan shi ne kashe wasu jami'an agaji bakwai a wani hari da wani jirgi mara matuki ya kai, lamarin da ya janyo tofin Allah tsine a duniya. To dai abu mafi muhimmanci a halin yanzu shi ne tsagaita bude wuta a Gaza, da kuma kawo karshen rikicin baki daya, wanda kasashen duniya ke ta yin kira da babbar murya.
Ya zuwa yanzu a zirin Gaza a kalla fiye da mutane dubu 33 sun rasa rayukansu dubbai sun bace cikin baraguzan gine-gine, yayin da sama da mutane dubu 75 suka jikkata, kuma kusan mutane miliyan 2.3 suna fuskantar matsanancin yunwa, kaso 80 cikin dari sun rasa matsugunansu.
Rashin tsagaita bude kowace rana yana kawo karin zubar da jini, karin barna, yunwa, cututtuka da hawaye. Miliyoyin mutane daga duk fadin duniya na ta zanga-zanga, suna kira ga a tsagaita bude wuta. Ana ta nanata kira ga ’yan siyasa da su kara himma, su yi duk mai yiwuwa don a daina kashe-kashen da ake yi a yanzu. Muryar kasar Sin na sama da ta kowace kasa game da tabbatar da an tsagaita bude wuta kuma an samu zaman lafiya a wannan yankin.
To ko da Isra'ila da Hamas sun amince da tsagaita bude wuta kuma aka wanzar da zaman lafiya, al'amuran yau da kullun ba za su koma yadda ya kamata a zirin Gaza cikin dogon lokaci ba. Ga Falasdinawa da ke zaune a can, babban hatsarin da za su fuskanta ba zai kasance Hamas ko Isra'ila ba kuma, sai dai na rashin gwamnati da za ta mulki yankin bisa nagartattun tsare-tsare.
Galibin masu ruwa da tsaki na Falasdinawa na kallon makomar yankin zirin Gaza bayan yakin ta fuskoki biyu. Da farko dai suna daukar Gaza wani lamari na cikin gida na Falasdinu da ke bukatar sassantawa tsakanin bangarori daban-daban na siyasar Falasdinawa kuma al'ummar Falasdinu su amince da shi.
Na biyu kuma, sun jaddada cewa Gaza ba za ta rabu da manyan manufofin siyasar Falasdinu ba, wadanda suka hada da ci gaba da gwagwarmayar neman 'yancin komawa da kuma 'yancin kai na kasa. (Sanusi Chen, Yahaya Mohammed, Faeza Mustapha)