logo

HAUSA

An kaddamar da kwamitin aiwatar da shirin gwamnati na tallata hajojin ta kafar intanet tare da karbar harajin bai daya a tarayyar Najeriya

2024-04-17 09:42:41 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da kwamitin aiwatar da shirin tallata hajojin da ake samarwa a Najeriya ta amfani da kafar sadarwar intanet tare kuma da sanya ido wajen ganin kamfanoni da ’yan kasuwa na biya haraji na bai daya ga gwamnati.

A lokacin da yake kaddamar da ’yan kwamitin ranar Talata 16 ga wata a fadarsa dake birnin Abuja, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, ana sa ran idan shirin ya kankama zai samarwa gwamnati kudin shigar da ya kai dala biliyan 2.7.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

An dai kirkiro da wannan shiri ne domin saukaka harkokin saye da sayarwa a zamanance kamar yadda yanzu haka yake faruwa a kasashen da suka ci gaba a fannin tattalin arziki a duniya.

Shugaba Bole Ahmed Tinubu ya ce, babu shakka Najeriya ta cancanci shiga cikin wannan tsari da jimawa, bisa la’akari da bunkasuwar da take samu a fagen kasuwanci a nahiyar Afrika da ma duniya baki daya.

Dandalin hada-hadar kasuwanci ta yanar gizo zai dangana da tasoshin jiragen ruwa, hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki ta yadda za a sami saukin kai komon mu’amullar ciniki a dan kankanen lokaci kuma cikin natsuwa da amuntaka.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ha’ila yau ya ce, wannan sabon tsari da za a fara amfani da shi, an kiyasta cewa zai takaita asarar dala biliyan 4 a duk shekara da Najeriya ke yi a sakamakon bin hanyoyi masu tsawo wajen kulla ciniki, kana da matsaloli na cin hanci da yake yawan wakana a tasoshin jiragen ruwan kasar.

“Shirin kasa na tallata hajoji ta yanar gizo ba wai an samar da shi ne ga ’yan Najeriya ba kadai, domin idan muka hade tsarinmu da sauran kasashen dake nahiyar Afrika za mu saukaka zurga-zurgar jiragen dakon kaya ta ruwa tare da inganta harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen dake nahiyar Afrika.”

An dai zabo wakilan kwamitin aiwatar da shirin daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati, kuma daga cikin fa’idojin shirin shi ne, sa’o’i 72 zuwa 48 da ake shafewa wajen fiton kaya a tasoshin ruwa za su dawo sa’a 24 ne kacal. (Garba Abdullahi Bagwai)