logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta hada karfin da hukumar UNESCO wajen kawo karshen tazarar karatu da ake samu a tsakanin jinsi

2024-04-16 10:27:32 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa, tana nan tana aiki tare da cibiyoyin bunkasa ilimi na kasa da kasa da kuma hukumar UNESCO domin tabbatar da ganin an kawo karshen tazarar karatu da ake samu tsakanin mata da maza a daukacin jihohin kasar.

Karamin minista a ma’aikatar ilimi Dr. Yusuf Sununu ne ya tabbatar da hakan a garin Suleja dake jihar Niger lokacin da yake bude taron karawa juna sani na yini biyar da aka shiryawa jami’an lura da ci gaban ilimin ’ya’ya mata da sauran masu ruwa da tsaki dake wasu daga cikin jihohin kasar, ya ce wannan yunkuri ana yinsa ne da zummar ganin an shigo da kowa a harkar neman ilimi ba tare da an bar wani jinsi a baya ba.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Karamin ministan ilimin a tarayyar Najeriya haka kuma ya ce, wannan yunkuri zai kai ga samun nasarar rage adadin yara miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya wanda kuma daga cikin wannan adadin kaso 60 mata ne.

Dr. Yusuf Sununu wanda ya kara jaddada kudirin ma’aikatarsa wajen sake daidaita al’amuran ilimi a kasar, kuma nasarar hakan kamar yadda ya fada za ta samu ne kawai muddin aka wadata iyaye mata da ilimi, inda ya nanata cewa, a bisa wannan turba ne yanzu gwamnatin tarayya ke ta kokarin neman tallafin hukumomin kasa da kasa da kuma hadin kan gwamnatocin jahohin kasar.

“Yanzu batun ilimi ya fi takaita ne kawai ga ’ya’ya maza adon haka akwai bukatar a kara inganta batun ilimin ’ya’ya mata.”

Karamin ministan ilimin na tarayyar Najeriya ya bukaci karin samun wayar da kai a game da muhimmancin ilimi ga ’ya’ya mace. Haka kuma ya yi kira ga masu ruwa da tsaki musamman a jihohin kasar da su rungumi tsarin amfani da sabuwar manufar ilimin ’ya’ya mata na kasa da gwamnati ta bullo da shi tare kuma da bin ka’idojin amfani da shi. (Garba Abdullahi Bagwai)