logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a kare tsaron na’urorin makamashin nukiliya

2024-04-16 10:41:20 CMG Hausa

 

Kwanan baya, an kai hari sau da dama a tashar samar da wutar lantarki mai amfani da makamashin nukiliya ta Zaporizhia ta kasar Ukraine. Jiya Litinin, kwamitin sulhu na MDD ya yi wani taro, inda bangarori daban-daban suka bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin. Inda Sin ta yi kira ga bangarori daban-daban da su kai zuciya nesa da kyautata mu’ammala da hadin gwiwa, kuma dole ne a tabbatar da matsayin kare tsaron na’urorin makamashin nukiliya daga tushe, don hana Bil Adama haddasa hadarin nukiliya.

Mataimakin wakilin dindindin dake majalisar Geng Shuang ya nuna cewa, Sin za ta ci gaba da ingiza shawarwarin samun kwanciyar hankali da taka rawar gani wajen magance rikicin Ukraine a siyasance.

Ban da wannan kuma, a taron da kwamitin ya yi a wannan rana kan halin da ake ciki a Yemen, Geng Shuang ya yi nuni da cewa, Sin ta yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki da su yi hakuri da juna da kuma hana tsanantar da halin da ake ciki, kuma tana goyon bayan bangarori daban-daban a Yemen da su gaggauta shimfida yanayi mai kyau ga warware rikicin a siyasance. (Amina Xu)