logo

HAUSA

An kunna wutar wasannin Olympics na lokacin zafi na 2024 na Paris

2024-04-16 20:06:47 CMG Hausa

Wutar gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi ta 2024 ta Paris, ta kama hanya bayan kunna ta da aka yi a mahaifar gasar wato tsohon garin Olympia dake kasar Girka, yayin wani bikin gargajiya da aka yi a yau Talata.

A cewar kwamitin shirya gasar Olympics na Hellenic na kasar Girka, kusan madauka wutan 600 ne za su yi tafiyar kilomita 5,000 a fadin kasar Girka, inda za su ratsa gomman birane da wuraren tarihi.

Za a mika wutar ne ga mashirya gasar Olympics ta 2024 ta Paris a ranar 26 ga watan Afrilun a filin wasa na Panathenaic na Athens, wurin da aka fara gudanar da wasannin Olympics na zamani a shekarar 1896. (Fa’iza Mustapha)